20 Yuni 2021 - 11:55
Iran: Shugaba Rouhani Ya Hadu Da Zababben Shugaban Kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Raouhani ya je ofishin Sayyid Ibrahim Ra’isi a ma’aikatar shari’ar kasar inda ya taya shi murnar zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya bayyana cewa Rouhani ya yi fatan alkhairi ga zababben shugaban kasar sannan ya kara da cewa zai fara shirye-shiryen mika masa shugabancin kasar kamar yadda aka tsara.

Sayyid Ibrahim Ra’isi ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a jiya Jumma’a da kuri’u fiye da miliyon 17,800,000 wanda kuma shi ne kashi 62 % na kuri’an da aka kada a zaben gaba daya.

342/